Barrister Turaki, wanda shi ne ministan ayyuka na musamman na Najeriya, yace su na samun ci-gaba a ayyukan da suke yi na shirya sulhu, domin su na samun hadin kai da taimakon ‘yan Najeriya. Ya ce da gaske ne akwai wasu mutanen dake fakewa da sunan wannan kungiya su na aikata wasu laifuffuka, kamar fashi a bankuna, amma kuma duk da haka ba zasu kasa iya gudanar da aikinsu ba.
Yace ganin irin nasarorin da suke samu, lallai hakar kwamitinsu zai kai ga cimma ruwa. Sai dai ya ki bayyana irin wadannan nasarorin da suka samu, yana mai fadin cewa yin hakan zai iya kawo cikas ga ayyukan da suke yi.
Ya yaba ma ‘ya’yan kwamitin, yana mai fadin cewa mutane ne masu kishi da kudurin wanzar da zaman lafiya a Najeriya.
Barrister Kabiru Tanimu Turaki, yana magana ne cikin wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka. Ga bayaninsa.