A taron da wakilin Muryar Amurka ya samu halarta mutane sun fadi albarkacin bakinsu domin halin tsaka mai wuya da suka ce sun samu kansu ciki. Ta dalilin dokar ko masu fitowa da suna sayen abinci su ci yanzu suna cikin zullumi domin rashin isasshen lokaci ta dalilin dokar takaita fita. Masu yin abinci da kafin dokar sukan tuka mudun shinkafa ashirin ko fiye da haka yanzu da kyar su sayar da mudu uku idan sun tuka. Masu sayen abincin na tsoron fitowa muddin yamma ta yi sabili da ukubar da jami'an tsaro ke ganawa mutane.
Wani abun da ya ba mutane mamaki shi ne wai ana doka amma kuma ana pasa shaguna. Ma'ana sace-sace da pasa gidajen mutane sun karu ainun karkashin dokar hana fita da daddare. Inji mazauna jihar lokacin da babu dokar ba'a fasa shaguna.Barayi sun karu fiye da kafin a aiwatar da dokar.
Wani abun da ya addabi mutanen kuma shi ne matasa fiye da dubu ashirin da suka yi asarar sana'ar sayar da katin wayar tafi da gidanka domin rufe kafofin sadarwa da jami'an tsaro suka yi a jihohin dake karkashin dokar ta baci. Ana zaton sabili da rashin aikin yi da matasa suka shiga shi ya haddasa karin barna da ake samu yanzu.
Wata matsala da ta kunno kai ita ce ta sha'anin kiwon lafiya. Yanzu babu likitan da zai amsa kiran gaggawa domin babu hanyar da za'a kira shi. Idan kuma an kira shi jam'an tsaro ka iya bata masa lokaci a hanya ta yarda kafin ya isa aibitin ta yiwu marasa lafiyan ya mutu. Haka mata masu juna biyu wasun su sun rasa rayukansu sanadiyar rashin samun kula da gaggawa lokacin da nakuda ta kamasu. An ce yara da dama sun mutu, musamman jariran da aka haifa a kauyuka sabo da matsala. Kafin iyayen su samu su kai asibiti yaro ya mutu. Mutane sun bayar da misalan yadda jami'an tsaro ke cin zarafin su ko dama suna cikin rigunan aiki kamar na masu kiwon lafiya.
Haka ma wasu suna ganin ba'a yi wa jiharsu adalci ba wajen kakaba mata dokar ta baci. Suna ganin babu wata hujjar saka masu dokar. Suna ganin sha'anin da walakin, wai goro a miya. Wasu kuma cewa suke gwamnati ba da gaske take neman sulhuntawa da kungiyar Boko Haram ba. Kamata ya yi bangarorin biyu su daina kashe-kashe su zauna kan teburin sulhu domin ba'a samun sulhu da cigaba da yaki.A bangaren gwamnati ya kamata ta nuna da gaske take yi domin su yan Boko Haram su yarda da ita.
Wakilinmu Ibrahim Abdulaziz na karin bayani.