Ganau sun ce mutane sun iso kauyen ne da asubahi jiya Talata a kan babura hamsin kowanne dauke da mutane biyu suka yi ma kauyen kawanya kana suka fara kashe mutane. Wasu da suka fito daga masallaci basu tsira ba. Bayan hakan maharan sun bi gida-gida suna fitar da mutane suna kashe wa.
Wadanda aka kashe sun hada da hakimin kauyen da limamin garin da kuma shugaban 'yan banga. Wadanda suka yi kokarin gudu basu tsira ba. Wani tsohon dan jarida Mainasara Dan Sarki ya tabbatar da cewa maharan sun kai dari kuma ana zaton makiyaya ne. Ya kara da cewa jami'an tsaro sun shiga neman wadanda suka aikata wannan aika-aikar. Lamarin ya sa Filani dake mazauna kusa kusa da kauyen suka arce domin tsoron kada a kaimasu ramuwar gayya. Haka kuma sun 'yan garin sun kaurace sun yi gudun hijira zuwa wasu wurare dalilin tsoron kada a sake kawo masu hari.
Gwamnan Jihar Alhaji Abduaziz Yari Abubakar ya zargi gwamnatin tarayya da gazawa a sha'anin tsaro. Dama can ita jihar ta sha fama irin wadannan hare-haren da mutuwar mutane da yawa.
Wakilinmu Mustafa Faruk Sanyinna na da rahoto.