Daya daga cikin jagororin makarantun Allo a jihar Kaduna, Sheik Salisu Abdullahi Mai Barota, yace “muna baiwa gwamna shawara, wadannan dokoki da yake aiwatarwa ba tare da ya tuntubi wadanda akema dokan ba, yayi gyara a cikin su.” Ya kuma ci gaba da cewa yakamata gwamnati da ware wanda suka mayar da bara sana’a, wanda basu alaka da almajiranci ta dauki mataki kansu wannan ba laifi.
Mai Barota, yace bai kamata ba a hana almajiri mai karatun Alkur’ani neman abinci, to mai zai ci yayi karatun? Sai dai in gwamnati ce zata dauki nauyin ciyar da dukkan makarantun tsangaya.
Shima dai shugaban kungiyar dalibai musulmi ta kasa shiyyar jihar Kaduna, Ustaz Sabi’u Shitu Bindawa, yace dokokin da ake fa basa jin ra’ayin al’umma. Inda yace damuwar su anan itace dokar bata girmama ra’yin al’umma ba musammam shugabannin addini.
Sai dai kuma shugaban kwamitin aikin Hajji da harkokin addinin musulunci a Majalisar Dokokin jihar Kaduna, Mohammad Lirwan Bawa, yace tun da dai su wakilan al’umma ne babu wata doka da zasu bari ta wuce ba tare da sunji ra’ayoyin al’ummar da suke wakilta ba.
Ya zuwa yanzu dai dokokin da gwamnatin Mallam Nasiru El-Rufa’I ta kawo wadanda suka fi jawo cece kuce a jihar Kaduna, sun hada da dokokin hana bara da tallace tallace da kuma dokar tsara yadda za a rika gudanar da wa’azi da kuma dokar haraji.
Your browser doesn’t support HTML5