Shugaba Buhari yace yana matukar tausayawa wadanda harin ya shafa tare da wadanda suka rasa dukiyoyinsu.
Shugaban ya ba babban sifeton 'yansanda da kuma hafsan hafsoshin Najeriya da su tabbatar da tsaro a yankunan da suke fama da hare-haren makiyaya kana su yi maganin duk kungiyoyin dake muzgunawa mutane a yankin.
Gwamnatin Najeriya ba zata cigaba da amincewa da aukuwar irin hakan ba,inji Buhari.
Kwamishanan 'yansandan jihar Enugu yace har yanzu suna binciken lamarin basu gama ba. Akan ko 'yansanda sun kama wani sai kwamishanan yace ba zai ce komi a kai ba domin basu gama bincike ba. Yace dole zasu yi abun da shugaban kasa da na 'yansanda suka fada masu. Suna nan suna yin iyakar kokarinsu.
Su ma abun da lamarin ya shafa sun bayyana ra'ayoyinsu. Wadanda aka zanta dasu sun yi maraba da matakin da shugaban kasa ya dauka. Suna fatan za'a gano wadanda suka aikata ta'asar domin a hukumtasu.
Su ma Fulanin da ake zargi da kai harin sun ce suna goyon bayan binciken domin a gano wadanda suke da hannu a aika-aikar domin kowa ya samu ya zauna lafiya.
Abubakar Isa Bauchi sakataren kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Enugu yace a yi bincike. Abun da suke bukata ke nan.
Ga karin bayani.