Janar Kazaure ya furta haka ne lokacin da ya kaiwa’yan gudun hijira da ke zaune a sansanin Damare na karamar hukumar Girei dake jihar Adamawa mai dauke da ‘yan gudun hijira sama da dubu biyu da dari uku dokin kayan abinci da magunguna tare da alkawalin aike da likita dan bautar kasa daya a sansanonin da ke jiha.
Ko wani shiri hukumar NEMA take yi domin karban baki yan gudun hijira daga makwabciya jumhuriyar Kamru dubu shida. shugaban hukumar kai dokin gaggawa na kasa da ke kula da jihar Adamawa Mal. Sa’ad Bello ya ce a halin da ake ciki yanzu hukumar ta maida sama da ‘yan gudun hijira dubu takwas sun koma muhallansu domin shirya tsugunar da su, kuma hukumomin da abin ya shafa suna gab da kammala karbar ‘yan gudun hijiran.
Ga karin bayani.