Wata kungiyar mata mai suna “Eye Opener” a turance ta ce rashin zaman lafiya da ke damun Najeriya siyasa ce.
Kungiyar, wadda ta yi tattaki a cikin garin Kaduna don nuna bukatar zaman lafiya na halin da ake ciki, ta ce akwai bukatar mutane su dage da yin addu'a.
A lokacin da shugabar kungiyar, Madam Magret Julius, ta kewa manema labarai karin bayani ta ce irin halin da ake ciki yanzu addu’a ce kawai mafita.
Shima jami’in ‘yan sandan da ya wakilci kwamishin ‘yan sanda jihar Kaduna, CSP Uzairu Abdullahi, ya ce irin wannan taro zai taimaka wajan tabbatar da zaman lafiya mai daurewa a Najeriya.
CSP Abdullahi ya kuma kara da cewa zaman lafiya hakki ne akan kowa ba na jami'an tsaro kadai ne ba.
Wasu mahalarta wannan tattakin zaman lafiya sun nuna damuwar su ganin yadda zamantakewa ta tabarbare yanzu, inda su ka buga misalai da yadda kiristoci da musulmai ke cudanya da juna a shekarun baya.
Taron tattakin zaman lafiyan da matan suka shirya dai sharar fage ne na ranar zaman lafiya ta duniya da Majalissar Dinkin Duniya ta ware ranar 21 ga watan satumbar Kowacce shekara da nufin nuna bukatar zaman lafiya a ko ina.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:
Your browser doesn’t support HTML5