Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara shari’ar Tsohon Kwamanda Manjo Janaral Hakeem Otiki


An kaddamar da shari’a ta musamman game da tsohon Kwamandan Rundunar Sojan Najeriya da ke jihar Sakkwato, Manjo Janaral Hakeem Otiki, bisa ga Sashi Na 8, kan zargin karkatar da makudan kudade da suka kai miliyoyin Nairori.

Shari’ar, wacce aka fara a babbar kotun soji da ke zama a ofishin Jami’in Sojoji, da ke Asokoro, an fara ta ne da misalin karfe 12:30 na yamma jiya Talata.

Babban Hafsan Sojoji ne ke jagorantar wannan shari’ar karkashin jagorancin Shugaban Rundunar Tsaro da Tsare-Tsare, ta hedkwatar sojojin Najeriya, Laftana Janar Lamidi Adeosun, wanda shi ne ma Alkalin kotun soji na musamman.

An tabbatar da cewar, an kama sojoji biyar da su ka yi batan dabo akan hanyar Sakkwato zuwa Kaduna, yayin da aka aike su da kudin a makon farko na watan Yuli na shekarar 2019.

Alkalin kotun soji na musamman, Laftana Janar Lamidi Adeosun, ya ce kotun ta samu hurumin yin wannan shari'ar ne bisa ga sashi na 131, karamin sashi na 101 na Dokokin Sojan Najeriya, da ke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Alkalin ya ba da tabbacin cewar, kotun za ta yi gaskiya da adalci yayin wannan shari’ar.

Wani lauyan tsarin mulki, Barista Yakubu Sale Bawa, ya ce, wannnan hobbasar da kudirin da Janaral Buratai ya yi aniya mataki ne mai kyau, kuma wannan ya nuna cewar Najeriya ta na kan tafarkin mulkin demokradiyya, da bin doka da oda. Shi ma Barista Mai Nasara Ibrahim Faskari, ya ce wannan mataki na hedikwatar sojan Najeriya ya dace da kundin tsarin mulkin kasa.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka daga Abuja, Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG