Gwamnatin jihar Nasarwa, ta bayana matakin da wasu ‘yan majalisar, dokokin jihar suka dauka na kin amincewa da nadin da babban Cif jojin jihar, Sulaiman Dikko, yayi domin bincikar zargin da akewa gwamna jihar, Umaru Tanko Almakura, a matsayin yashin sani doka.
Wasu ‘yan majalisar dokokin jihar, Nasarawa suka yi wata zama a garin karu a cikin jihar, suka zartar da hukuncin rashin amincewa da kwamitin mutane bakwai da Cif jojin jihar ya nada don binciken zarge-zarge goma sha shida da akewa gwamna jihar.
Mai Magana da yawu gwamnatin jihar Nasarawa, Abdulhamid Yakubu Kwara, yace zaman da ‘yan majalisar suka yi a wani wuri ba’a majalisa ba baya bisa ka’ida.
Shi kuwa shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin na jihar Nasarawa, Muhammad Baba Ibaku, cewa yayi majalisar na da yancin tayi zama a duk inda taga ya dace.
Your browser doesn’t support HTML5