Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Goyon Bayan Gwamna Nasarawa


Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa.
Gwamna Tanko Al-Makura na Jihar Nassarawa.

Zanga-zangar ta kara haddasa cunkoson a babban hanyar zuwa Nasarawa.

Magoya bayan gwamna Umaru Tanko al-Makura na Jihar nassarawa, sun yi wata zanga-zanga yau laraba a garin Mararraba dake dab da shiga Abuja, babban birbnin tarayyar Najeriya, domin su nuna fusata da rashin yarda da matakan da 'ya'yan jam'iyyar PDP mai rinjaye a majalisar dokokin jihar ke dauka na neman tumbuke shi daga kan kujerarsa.

Zanga-zangar ta kara haddasa cunkoson ababen hawa a wannan wurin da ya saba ganin cunkoso a duk ranar aiki.

Wani kansila a yankin, Usman Abdullahi, ya zargi shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, da hannu a wannan abinda ya kira makarkashiyar PDP ta neman tsige gwamna al-Makura. Yace al'ummar da suka zabi gwamnan, ba sune suke neman tsige shi ba.

Yace zasu dauki dukkan matakan da zasu iya domin nunawa 'yan majalisar dokokin jihar Nassarawa cewa su na kaunar gwamnansu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG