Rashin Kammala Ayyuka Shi Ne Illa A Nijeriya

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathn

Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilan Nijeriya kan Zirga-zirgar kasa, Honorabul Musa Sarkin Adar yayi takaicin yadda gwamnatocin Nijeriya ke kin kammala ayyukan da su ka tarar, al’amarin da ya ce na janyo asarar kudi mai yawa da kuma hana jama’a amfana da ayyuka masu muhimmanci saboda kawai gwamnatin da ta shude ce ta fara.
A hirarsu da Jummai Honorabul Musa Sarkin Adar y ace wani sa’in kuma su ma mutane da nasu. Su kan kalli ayyukan gwamnati ne ta fuskar wanda ya fara. Hakan, in ji shi kan sa wasu gwamnatocin su kirkiro nasu ayyukan, wanda hakan kan janyo rashin kudi da asarar da kuma watsi da muhimman ayyuka.

Yace hanzu haka ma akwai wasu ayyukan da aka fara tun a gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ba a kammala ba duk kuwa da an san sun a da muhimmanci sosai. Yace kuma a zaman in ‘Yar’aduwa an fara yashe kogin Niger amma kuma sai aka daina da gwamnatin Goodluck ta hau gadon mulki.

Yace an kashe kudi mai yawa a aikin kafin aka dakatar kuma yashin da aka yashe na iya dawowa ta yadda kudin da aka kashe wajen yasar zai zama asarar.
Dan Majalisar y ace ko gwamnatin marigayi Abacha ma ta sayo jiragen sama da dama amma sai aka ki fara aiki da su cikin lokaci saboda kawai wata gwamnatin ce ta fara.

To amma da yake amsa wata tambaya Hon Sarkin Adar y ace zai nemi hadin kan ‘yan kwamitin don ganin an kafa doka ta talasta gwamnatoci su kammala ayyukan da gwamnatocin da su ka gabata su ka fara.

Al’amarin da ya ce na janyo asarar kudi mai yawa da kuma hana jama’a amfana da ayyuka masu muhimmanci saboda kawai gwamnatin da ta shude ce ta fara.

A hirarsu da Jummai Honorabul Musa Sarkin Adar y ace wani sa’in kuma su ma mutane da nasu. Su kan kalli ayyukan gwamnati ne ta fuskar wanda ya fara. Hakan, in ji shi kan sa wasu gwamnatocin su kirkiro nasu ayyukan, wanda hakan kan janyo rashin kudi da asarar da kuma watsi da muhimman ayyuka.

Yace hanzu haka ma akwai wasu ayyukan da aka fara tun a gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ba a kammala ba duk kuwa da an san sun a da muhimmanci sosai. Yace kuma a zaman in ‘Yar’aduwa an fara yashe kogin Niger amma kuma sai aka daina da gwamnatin Goodluck ta hau gadon mulki.

Yace an kashe kudi mai yawa a aikin kafin aka dakatar kuma yashin da aka yashe na iya dawowa ta yadda kudin da aka kashe wajen yasar zai zama asarar.

Dan Majalisar y ace ko gwamnatin marigayi Abacha ma ta sayo jiragen sama da dama amma sai aka ki fara aiki da su cikin lokaci saboda kawai wata gwamnatin ce ta fara. To amma da yak e amsa wata tambaya Hon Sarkin Adar y ace zai nemi hadin kan ‘yan kwamitin don ganin an kafa doka ta talasta gwamnatoci su kammala ayyukan da gwamnatocin da su ka gabata su ka fara.

Your browser doesn’t support HTML5

Yawan Watsi Da Ayyukan Gwamanti