Kwamishinar ayyukan kiwon lafiya ta Jihar, Dr. Salma Anas-Kolo, ta dora laifin bullar Polio da yawa haka a jihar a kan halin rashin tsaron da ake fama da shi a akasarin yankunan jihar, abinda ya sa ake fuskantar matukar wahala wajen gudanar da ayyukan rigakafi ga wadanda ke cikin hatsarin kamuwa da cutar.
Kwamishinar ta ce wannan adadi na yara 14 sabbin kamuwa da Polio, ya zarce na kowace jiha a Najeriya inda ya zuwa yanzu aka samu mutane 37 a fadin kasar.
Dr. Anas-Kolo tana magana ne a wurin taron da aka kira na sarakunan gargajiya na fadin jihar, domin zaburar da su game da shawo kan jama'a ta yadda za a iya jan burki ga yaduwar cutar.
Ta yaba ma ma'aikatan kiwon lafiya wadanda ta ce ba domin su ba, da adadin wadanda suka kamu da cutar ya fi haka, domin sun sadaukar da kawunansu, suka shiga wuraren da ke da hatsarin gaske domin su ba yara maganin rigakafin.
Mai martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Garbai al-Amin Elkanemi, wanda ya karbi bakuncin wannan taron sarakunan gargajiya a fadarsa, ya roki al'ummar kasarsa da su rungumi wannan shirin su ba 'ya;yansu masu shekaru biyar zuwa kasa magungunan rigakafin cututtuka biyar da suka fi kashe yara.
Ya roki dukkan majalisun sarautun gargajiya na jihar da su kara zage damtse wajen yakar Polio, yana mai cewa babu ta yadda gwamnati zata ba su wani maganin da zai cutar da su.