Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bangarorin Jam'iyyar PDP Sun Dambace A Majalisa


Alamar PDP
Alamar PDP

Rigimar bangaranci a jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya ta dau wani sabon salo, ta yadda sai da bangarorin su ka ba hammata iska a Majalisar Wakilan Nijeriya

Bayan bude Majalisar Wakilan Nijeriya, sai Kakakin Majalisar Aminu Waziri Tambuwal ya karanata wa Majalisar wata takardar neman damar ziyartar shugabannin Majalisar. Aka kuwa gabatar da Shugaban sabon bangaren na PDP ga Majalisar, sai nan da nan ‘yan bangaren Bamanga Tukur bisa jagorancin Dan Majalisa Nado Karibu daga jihar Bayelsa su ka yi ca; aka shiga bai wa hammata iska har aka yaga ma Honorabul Dakuku Peterside dan jihar Rivers tufafi.

Daya daga cikin ‘yan bangaren Baraje a Majalisar mai suna Alhassan Ado Doguwa ya gaya wa wakiliyarmu a Majalisar Madina Dauda cewa sun kai ziyarar ce saboda su yi wa ‘yan Nijeriya yadda su ke so a kuma lokacin da ya dace. To saidai, wani jigon bangaren Baraje kuma gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce fadan da aka yi a Majalisar ba wani bakon abu ba ne a dimokaradiyya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:10 0:00
Shiga Kai Tsaye

Gwamna Lamido ya gaya ma Madina cewa har a Amurka ma akan yi fada a Majalisa. Haka ma a Burtaniya da Indiya da Afirka Ta Kudu da sauransu. Madina ta ce bangaren na Baraje na kara samun magoya baya.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG