Ibrahim Lamorde yace duk yadda aka ce za'a yi idan ba kotuna sun yanke hukuncin daure mutum ba da wuya mutane su amince da yadda ake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
Iyakacin abun da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ko EFCC zata yi shi ne ta kama mutum, ta bincikeshi ta kaishi kotu. Duk wata dabara kuma ta danganta da yadda kotu ta yanke hukunci. Babu wanda zai sa kotu tayi abun da bata son tayi.
Amma inji Ibrahim Lamorde, yana ganin abubuwa zasu canza kwanan nan a kotunan Najeriya.
Shugaban hukumar ya musanta zargin sa 'yan adawa a gaba da kuma barin wadanda ke yin mulki suna cin karensu ba babbaka. Yace matukar ba'a samu nasarar shari'un cin hanci a kotun ba zai yi wuya a fahimci jajircewar hukumar. Yace duk yadda aka yi idan ba'a daure mutum ba an bashi lokaci ya zauna gidan yari to duk aikin banza ne. Ba'a ce komi ba. Idan an kama mutum kana a bashi beli sai ya cigaba da rayuwarsa kuma babu abun da ya canza. Idan an kaisu kotu sun samu beli sai su daukaka kara laoyoyinsu su dainga jan lokaci.
Masu sharhi dai na ganin kanwar cin hancin dai ja ce a tsakanin duka la'in 'yan Najeriya da ya zama wajibi hukumomi suke gwada misali daga kawunansu matukar za'a amince da yaki da cin hancin.
A taron kasa Dr Junaidu Muhammed yace malaman Najeriya da sarakunan duk sun zama 'yan kama. Babu wanda ya amince dasu domin an san zancen banza suke yi. Duk wanda aka gani yana jawo malamai ko fada fada kusa dashi ba domin kasar yake yi ba yana da wata manufa ta siyasa ce. Kasar ta lalace. Malamai sun zama 'yan kasuwa. Sarakuna sun zama 'yan kwangila. Talakan Najeriya bai tsinci komi ba sai azaba da rashin mutunci da rashin wuta da dai sauransu.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka.
Your browser doesn’t support HTML5