Babban kalubalen da ke ci mana tuwo a kwarya bai wuce yadda al’ummar gari basa mara wa mawaka baya ta yadda basa zuwa wuraren da suke wasa kuma suke ganin kyashin zuwa kallonsu a cewar Ralph John, wanda aka fi sani da Don R.
Matashin ya bayya cewa sai ka ga an kawo wasu mawaka daga wasu garuruwan Nijeriya amma abin mamaki sai mutane su rika tururwar zuwa kallonsu ba tare da la’akari da ko nawa zasu biya ba.
Don R, ya ce hakan na ci masu tuwo a kwarya tare da sanyaya musu gwiwa da kan basu rashin kuzarin yin wasannin kamar sauran mawaka.
Ralph John, ya ce abin takaici ne yadda ba’a sayen fayafayensu a kasuwanni, kuma ga irin illar da masu satar fasaha ke yi masu musamman yadda suke satar wokoki ta wayoyin saluluarsu
Daga karshe ya kara da cewa fatan sa dai bai wuce ya zamo kamar su 2face, da Psquare, da sauransu ba, ya kuma ce ta dalilin waka ya zaga wasu daga cikin kasashen Africa.
Your browser doesn’t support HTML5