Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Batun Daidaito Tsakanin Maza Da Mata


Taron mata
Taron mata

A yau dandali zai waiwaye batun nan da kungiyoyi da masu kare hakkin bil Adama ke tafka muhawara akan daidaito tsakanin maza da mata.

Wannan daidaito dai ka iya kasancewa na ilimi zamantakewa ko rike madafan ikon, akan haka ne wakiliyar Dandalin voa, Baraka Bashir, ta zanta da wasu mata dangane da wannan batu na daidaito.

Malama Aisha Mahmud, tace ta amince da daidaiton Mace da na Miji, ta fuskar ibada, da kuma duk wani kokari da Mace zatayi domin neman na kanta da kuma neman rike madafan iko.

Ita kuwa Malama Zainab Abdulraham, cewa tayi bata amince da daidaito tsakanin Maza da Mata ba saboda a cewarta ba kowane abu bane da dan namiji zai yiba ne ‘yar mace zata yiba domin kuwa su mata suna da rauni.

Daga karshe matan sun yi ittifaki cewa tauye mata da akeyi a al’umar shi yasa matan suka koma baya basu ganin cewa zasu iya yin abinda namiji zaiyi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:03 0:00

XS
SM
MD
LG