Rasha tace ba za a tura dakarun kasa da kasa Siriya ba

Masu zanga zangar kin jinin shugaba Bashar al-Assad na kasar Siriya

Rasha wadda ta kasance babbar abokiyar kawancen Syria ce tace ko kusa ba zata bari a tura sojojin kasashen waje cikin kasar Syrian ba.

Rasha wadda ta kasance babbar kawar Syria tace ko kusa ba zata bari a tura sojojin kasashen waje cikin kasar Syrian ba. Rasha ta bayyana haka ne yayinda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yake muhawara kan hanyoyin shawo kan rikicin da ya kai wata 10, na nuna rashin amincewa da mulkin shugaba Bashar al-Assad.

Da yake magana kan wannan batu yau laraba, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, yace kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ba zai goyi bayan duk wani mai niyyar amfani da karfi kan Syria ba

Ya bayyana haka ne kwana daya bayanda manyan jami’an difilomasiyya a kwamitin sulhun suka zauna domin nazari kan daftarin da Rasha tayi wa kwaskwarima, har take cewa za a dora alhakin rikicin kasar ta sham kan gwamnati da kuma ‘yan tawaye. Amurka, da Faransa, da Britaniya suna neman kwamitin ya zartas da kuduri mai karfi da zai soki lamirin gwamnatin Syria, amma Rasha da China sun ki.

A jiya talata Syria tayi watsi da shawarar da Qatar ta bayar, na neman a tura sojojin ketare a Syria domin shawo kan zubda jini da ake yi, Syria tana cewa hakan zai kara dagula lamarin, kuma ya bada kafa ga kasashen waje suyi katsalandan a al’amuran kasar.

Shugaban Amurka Barack Obama a jiya talata yayi Allah wadai da ci gaba da matakan murkushe masu zanga zanga da hukumomin Syria suke yi, ya kuma yi alkawrin kara azamar kasa da kasa na tilastawa shugaba Assad yayi murabus.