Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta A Syria


Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton
Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton

Ta kuma janye sauran ma'aikatan jakadancinta da suka rage a kasar tana mai bayani da kara tabarbarewar tsaro.

Amurka ta rufe ofishin jakadancinta dake kasar Sham , ko Syria, sannan ta janye sauran ma'aikatan diflomasiyyarta dake can tana mai bayani da kara tabarbarewar tsaro a kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fada yau litinin cewa an dakatar da dukkan ayyukan ofishin jakadanci a kasar, kuma jakada Robert Ford da sauran ma'aikatan diflomasiyya sun riga da sun bar kasar. A watan da ya shige Amurka ta yi gargadin cewa zata rufe ofishin jakadancinta dake Damascus, sai fa idan gwamnatin Sham ta takali batun damuwar tsaron lafiyar ma'aikata tana mai misali da tashe-tashen bama-bamai a motoci cikin 'yan kwanakin nan.

Wannan matakin na kara mayar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad saniyar ware a saboda matakan babu sani babu sabon da take dauka na murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati, yana zuwa a daidai lokacin da gwamnatin ta Sham take kara daukar matakan kai farmaki a wasu biranen kasar.

'Yan rajin kare hakkin bil Adama sun ce an kashe mutane akalla 24, wasu da dama suka ji rauni, a lokacin da dakarun gwamnati suka kaddamar da wani gagarumin farmaki a kan birnin Homs inda ake nuna turjiya.

A yau litinin, gidajen telebijin na tauraron dan Adam na kasashen larabawa sun nuna hotunan hayaki na tashi sama daga gine-ginen da aka lalata a birnin Homs. An kai hare-haren a unguwanni da dama na wannan birni, inda wani bututun man fetur ma yayi bindiga.

Gidan telebijin na kasar ta Sham yace kungiyoyin 'yan ta'adda ne suka tayar da wadannan bama-bamai.

Babu dai wata kafa mai zaman kanta ta tabbatar da sahihancinb mace-mace a kasar a saboda gwamnatin Sham tana takaita labarai dake fitowa daga kasar.

XS
SM
MD
LG