Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Wakilin Muryar Amurka A Pakistan


Marigayi Mukarram Khan Aatif a bakin aikinsa
Marigayi Mukarram Khan Aatif a bakin aikinsa

Talatar nan aka kai farmaki kan Mukarram Khan Attif, wakilin Deewa Radio na Muryar Amurka, lokacin da yake salla cikin wani masallaci a kusa da gidansa a garin Shabqadar.

'Yan bindiga a arewa maso gabashin Pakistan sun kashe wani dan jarida wakilin Muryar Amurka.

Talatar nan aka kai farmaki kan Mukarram Khan Aatif, wakilin Deewa Radio na Muryar Amurka, lokacin da yake salla cikin wani masallaci a kusa da gidansa a garin Shabqadar. Wannan gari yana mai tazarar kilomita 35 daga birnin Peshawar, babban birnin lardin Khyber-Pakhtunkhwa.

'Yan sanda a garin suka ce wasu mahara guda biyu a kan babura sun je wannan masallaci a lokacin da ake sallar Isha. Daya daga cikinsu ya shiga cikin masallacin, ya harbi Aatif a kai, sannan ya gudu.

An garzaya da Aatif zuwa asibiti, amma daga bisani sai rai yayi halinsa.

Wani mai magana da yawun kungiyar Taliban ta Pakistan, ya fadawa 'yan jarida cewa kungiyarsu ce ta kashe Aatif.

Abokan marigayin sun fadawa Muryar Amurka cewa a can baya, tsagera sun sha yin barazanar kashe shi. Ala tilas shi da iyalinsa suka gudu suka koma Shabqadar daga garin Mohmand a saboda irin wannan barazana da ake yi masa.

'Yan rajin kare hakkin aikin jarida a Pakistan sun yi Allah wadarai da kisan Aatif su na kuma sukar gwamnati a saboda ba ta daukar matakan da suka kai kima na kare 'yan jarida.

A shekarar 2011 da ta shige, an kashe 'yan jarida guda 10 a kasar Pakistan.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG