Rasha Ta Kai Harin Da Ya Halaka Mutum 28 A Ukraine

Babban birnin Ukraine, Kyiva ranar Yuli 8, 2024, bayan harin Rasha

Wani babban harin makami mai linzami da Rasha ta kai a Ukraine ya kashe akalla mutum 28 tare da jikkata kusan 100 a ranar Litinin, kamar yadda jami'ai suka ce.

Wani makami mai linzami ya fada wani babban asibitin kananan yara a Kyiv, babban birnin kasar.

Yuli 8, 2024 a Kyiv, na nuna motoci suna konewa bayan wani hari da makami mai linzami da Rasha ta kai.

Harin na rana da Rasha ta kai dauke da makamai masu linzami iri daban-daban sama da 40, ya auna garuruwa biyar na Ukraine inda suka afkawa gine-ginen gidaje da ababen more rayuwa, in ji shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy a wani sakon da ya wallafa a dandalin sada zumunta.

Hare-haren da aka kai a Kryvyi Rih, mahaifar Zelenskyy a tsakiyar Ukraine, ya kashe mutum 10 tare da raunata 47, a wani abin da shugaban hukumar birnin, Oleksandr Vilkul, ya ce harin makami mai linzami ne. Hukumomi sun ce an kashe mutane bakwai a Kyiv.

Russia-Ukraine

"Yana da matukar muhimmanci kada duniya ta yi shiru game da wannan lamarin a yanzu kuma kowa ya ga yadda Rasha take da kuma abin da take yi," in ji Zelenskyy a kan kafofin watsa labarun.

Shugabannin kasashen yammacin duniya da suke marawa Ukraine baya a yakin na gudanar da taron kwanaki uku na kungiyar tsaro ta NATO a birnin Washington daga ranar Talata inda ake sa ran batun mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine zai kasance muhimmin batu a taron.

-AP