Yayin da ake bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya, Jamhuriyar Nijar ta bi sahun takwarorinta na duniya domin karrama wannan rana, inda Malam Mahamadu Lawali Danda, ministan sadarwa na kasar, yayi jawabi a kafofin yada labarai na gwamnati a madadin hukumomin kasar don bayyana wa ‘yan Nijar irin matakan da gwamnati ke dauka domin kara inganta aikin jarida da ke bai wa 'yan kasar damar fadin albarkacin baki bisa tafarkin dimokaradiyya.
“Zagayowar wannan ranar na zuwa ne a daidai lokacin da aka fidda sunayen sabbin magabatan hukumar sadarwa ta kasar da zasu share shekaru 5 suna daidaita aikin ‘yan jarida,” a cewar Lawali.
Ya kara da cewa, gwamnatin Nijar tun daga shugaban kasa zuwa Firai Minista bisa tsarin ayyukan gwamnati na shekaru 5, ta dauki matakan saita aikin jarida ta hanyar yin sabbin dokoki da zasu gyara fannin da ma sake raya yanayin aiki na kafofin yada labarai na gwamnati da masu zaman kansu, tare da girka sabbin na'urorin da zasu sa a kama talabijin a saukake.
Da yake jawabi a wani taro albarkacin ranar ta ‘yancin 'yan jarida, Alhaji Mati shugaban hukumar kare hakkokin bil’adama ta Jamhuriyar Nijar, ya ce babu maganar dimokaradiyya in dai babu ‘yancin ‘yan jarida.
“Idan muka tabo aikin jarida, wanda a yau muke tunawa da ranarsa, aikin na da nasaba da ‘yancin fadin albarkacin baki da ke zama wani ginshikin tabbatar da dimokaradiyya.
Sai dai aikin na ‘yan jarida na cin karo da matsaloli da dama da ‘yan jaridar ke fuskanta.
Musa Arzuka, dan jarida ne a Birni N’Konni, ya ce rashin kyakkyawan yanayin aiki na daga cikin kalubalen da suke fuskanta, kuma gwamnati ba ta cika maida hankali wajen tallafa wa ‘yan jarida ba.
Duk da samun ci gaba mai yawa a fannin aikin jarida a jamhuriyar Nijar ana iya cewa da sauran runa a kaba, duba da irin matsalolin da ‘yan jaridar ke fama da su da hukumomi suka kasa warwarewa.
Saurari cikakken rahoton Harouna Mamane Bako:
Your browser doesn’t support HTML5