Yau ranar 12 ga watan Mayu ake bikin tunawa da ma’aikatan jinya a fadin duniya.
WASHINGTON D.C. —
Kamar ko ina a fadin duniya kasar jamhuriyar Nijar ta gudanar da bikin tunawa da ma’aikatan jinya, inda ministan kiwon lafiya Idi Iliyasu Mainasara yiwa al’ummar kasar jawabi a madadin gwamnatin kasar.
A cewar ministan aikin ma’aikatan jinya yana da muhimmanci sosai ga kiyaye hakkin bil adama. Maudu’in bana shine yadda za a ingantawa ma’aikatan jinya ta yadda zasu cimma nauyin da ya rataya a wuyansu.
Ma’aikatan jinya na taka rawa matuka wajen kula da lafiyar al’umma a asibitoci da cibiyoyin kula da lafiya a fadin duniya.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Mamman Bako.
Your browser doesn’t support HTML5