A ranar Talata ake sa ran tsohon shugaban Amurka Donald Trump zai gurfana a gaban kotu a birnin New York.
Gurfanar Trump a gaban Alkali, zai zamanto na farko da za a ga wani tsohon shugaban kasa ya yi a tarihin Amurka.
A ranar Juma’a hukumomi kotun, suka tabbatar da cewa tsohon shugaban na Amurka zai bayyana a gaban Alkali, bayan da masu taimakawa Alkali a ranar Alhamis suka ce Trump ya aikata ba daidai kan zargin da ake masa na biyan wata mai shirya fina-finan batsa kudin toshiyar baki, don ta yi shiru kan mu’amullar da suka yi kafin ya zama shugaban kasa – zargin da Trump ya sha musantawa.
Ana sa ran idan Trump ya mika kansa a ranar Talata, za a masa daidai da yadda ake yi wa duk wani laifi, inda za a dauki hotonsa da hotunan yatsunsa.
Bayanai sun yi nuni da cewa ba za a saka masa ankwa ba, amma zai kasance tare da masu kare lafiyarsa. Ana kuma sa ran a ranar za a bar shi ya tafi gida.
Da yawa daga cikin ‘yan Republican da shi kansa Trump sun kwatanta wannan shari’a a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa.
“Ta ce na zaku na ga irin sabbin hujjojin da suka tattara bayan kusan shekara goma, koma dai mene ne, wannan ba wani abu ba ne illa bi-ta-da-kulli tun da an sha yin shari’a kan wannan batu.” In ji Alina Habba, daya daga cikin lauyoyin da za su kare Trump a wannan shari’a.