Hajiya Hadiza Ali Dagabana wacce ke zama darektar hukumar bada katin zama dan kasa ta bayyana wa Muryar Amurka a wata hira ta musamman cewa, an kara lokacin yin wannan aiki zuwa ranar 19 ga watan Janairun shekarar 2021 mai kamawa.
Ta ce ma’aikata a hukumarta suna nan suna aiki dare da rana a ofisoshin su na jihohin da na kananan hukumomi don su tabbatar da duk mutanen da suka neman rubuta sunayen su an yi musu rajista.
Duk da cewa dimbin mutane ke zuwa domin rubuta sanuayen su, hukumar nada adadin mutane da ta kayyade tana rubuta sunayen su a duk rana.
Hajiya Hadiza ta kara da cewa wadanda basu samu damar rajista a ranar da suke je ofishin rubuta sanayen, ana basu lambobi dan su dawo waye gari domin an yi musu rajista. Mutane na ci gaba da kwarara a ofisoshin hukumar bada katin zama dan kasa.
Tuni hukumar ta yiwa sama da mutum miliyan 44 rajistan zama dan kasa a fadin kasar kana tana hasashen yiwa mutum miliyan 45 rajista a cikin lokaci kalilan.
Darektar ta NIN, ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi kokarin su yi rajistan lambobin wayoyin su kafin ranar 19 ga wata Janairun shekarar 2021, haka zalika wadan basu da rajista da hukumar NIN su yi haka kafin lokacin da aka kayyade na ranar 9 ga watan Faburairun 2021.
Ta ce hukumarta ta baiwa kamfanoni 178 lasin rubuta sunayen mutane da zasu shiga ko ina a cikin kasar a cikin mako biyu masu zuwa su yiwa mutane rajitsa.
Ta ce a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ba sai mutum ya je ofishin hukumar NIN kafin ya yi rajista saboda kamfanonin da aka basu lasin zasu bi mutane gida gida suna musu rajista.
Ga dai tattaunawa da Medina Dauda ta yi da Hajiya Hadiza:
Your browser doesn’t support HTML5