Rana Ta Musamman Don Kula Da Lafiya Da Kuma Tsaftar Baki Ta Duniya 2024

World Oral Care Day

Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 20 ga watan Maris na kowacce shekara a matsayin ranar kula da lafiya da kuma tsaftar baki ta duniya.

An fara ayyana ranar kula da lafiyar baki da hakora ne a shekarar 2007 amma ba a fara bikin ranar ba sai a shekarar 2013..

Wasu yan Najeriya sun yi bayani kan irin hanyoyin da suke bi wajen kula da tsaftar bakinsu.

Taken ranar na wannan shekarar shine ‘Jin dadin bakin ka shine jin dadin jikin ka.

.

An ware ranar ce don wayar da kan jama’a kan yadda za su kula da tsaftar bakinsu don guje wa cututtuka da ka iya shafar baki ko hakori.

Kwararren likitan hakori Dr. Mustapha Danjuma Abubakar na ma’aikatar lafiya ta gwamnatin tarayyar Najeriya ya bayyana irin cututtukan hakori da aka fi cin karo da su musamman a Najeriya.

Sakataren kungiyar ma’aikatan lafiya masu kula da tsaftar baki ta Najeriya (ASSODENTHSA) Kwamred Yasinu Khalil yayi karin bayani game da muhimmancin wannan rana da kuma irin ayyukan da su ke yi a irin wannan ranar.

Kwamred Yasinu ya kara da bayyana wasu matsaloli da rashin kula da tsaftar baki da hakori ka iya haifar wa.

Ranar dai wata dama ce ta zuwa asibitin hakori don a duba lafiyar hakori kyauta.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rana Ta Musamman Don Kula Da Lafiya Da Kuma Tsaftar Baki Ta Duniya 2024