Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Rediyo Ta Duniya: Muryar Amurka Ya Samu Karramawa Da Jinjina


Lambar Yabo da Kungiyar Marubuta da Masu Saurarran Rediyo ta bawa Muryar Amurka
Lambar Yabo da Kungiyar Marubuta da Masu Saurarran Rediyo ta bawa Muryar Amurka

A daidai lokacin da duniya ke bikin ranar rediyo ta duniya, muna alfahari tare tayamu murnar gane irin gudunmowar da Sashen Hausa na Muryar Amurka yake bayarwa ga aikin jarida da kuma rawar da wakilanmu ke takawa wajen ilmantarwa da fadakar da al'ummar duniya.

A yau, Laraba, 13 ga watan Fabrairu da mu ke ciki, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya samu lambar yabo daga Kungiyar Marubuta da Masu Sauraran Rediyo ta Jihar Adamawa a wani kwarya-kwaryan biki daya gudana a ginin Cibiyar 'Yan Jaridu ta birnin Yola.

Kamar yadda sakon dake rubuce a allon lambar yabon ya nuna, "wannan jinjina ce ga irin gudunmowar da Sashen Hausa na Muryar Amurka ke bayarwa wajen bunkasar aikin jarida da sauraran rediyo."

Bugu da kari, a yau wakiliyarmu ta babbar birnin jihar Filato, Jos, Zainab Babaji ta lashe kyautar duniya ta Rediyon Manoma ta Liz Hughes ta bana saboda rahotannin kasa da kasa da take turawa da kuma shahararren shirin nan da take gabatarwa me tattauna al'amuran yau da kullum me suna "Wake Daya" a tashar rediyo ta "Peace FM" ta jihar Filato dake yankin arewa maso tsakiyar Najeriya.

Wakiliyar Muryar Amurka a jihar Filato, Zainab Babaji
Wakiliyar Muryar Amurka a jihar Filato, Zainab Babaji

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG