Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Mata Ta Duniya: Gwamnatina Zata Bada Fifiko Akan Walwalar Mata-Tinubu


Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu

Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu, ya sha alwashin cewar gwamnatinsa zata bada fifiko kan walwalar mata da kiyaye hakkokinsu tare da bunkasa rayuwarsu.

WASHINGTON DC - A sanarwar da hadiminsa akan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar game da zagayowar ranar mata ta duniya, Tinubu ya bayyana mata a matsayin kashin bayan cigaban kowace al’umma.

Shugaban kasar wanda ya fayyace irin rawar da mata ke takawa wajen gina al’umma, ya jaddada cewar, babu shakka, matan Najeriya sun bada gudunmowa wajen bunkasa, cigaba da kuma daukakar kasar.

A cewar sanarwar, “Shugaba Tinubu ya bada tabbacin cewar a kowane bangare na ci gaban dan adam, irin zarar da matan Najeriya suka yi shaida ce ta jajircewa da karfin hali da fikira ta dukkanin matan duniya, kuma wata alama ce ta nagartaccen wakilci na kyakkyawan fata da wanzuwar al’amura.

Tinubu ya kara da cewar, taken bikin ranar mata ta duniya na bana na, “a zuba jari a mata domin hanzarta ci gaba”, ya dace da manufofin da gwamnatinsa ta kirkira akan ilmi da baiwa mata tallafi, ba wai kawai ta hanyar shigo dasu a harkar mulki ba, harma da tabbatar da cewa sun ci gaba da zama murya mai mahimmanci a fannin ci gaba a dukkanin bangarorin tattaliin arziki.

Hakazalika Shugaba Tinubu yace, “gwamnatinsa ta maida hankali wajen zuba jari a fannin ilmin ‘ya’ya mata, tare da kirkirar tsare-tsaren da zasu karfafesu wajen bada gudunmowa a fannonin ilmi da kimiya da fasaha da bincike da kirkire-kirkiren da zasu yi tasiri a nan gaba”.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG