Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Ranar Mata Ta Duniya Cikin Hotuna

Bikin ranar mata ta duniya
Bikin ranar mata ta duniya

Taken wannan shekara shi ne “kwadaitar da jama’a” wajen mayar da hankalinsu kan al’amuran da suka shafi saka mata a harkokin yau da kullum.

Takwas ga watan Maris din kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin nazari kan irin nasarori da mata suka samu a sassan duniya da kuma kalubalen da suke fuskanta.

Ko da yake, an dade ana bikin ranar ta mata, amma sai a shekarar 1975 Majalisar Dinkin Duniya ta rungumi wannan rana a hukumance.

Taken wannan shekara shi ne “kwadaitar da jama’a” wajen mayar da hankalinsu kan al’amuran da suka shafi saka mata a harkokin yau da kullum.

Muhimman batutuwan da akan tabo a wannan rana da ake binkinta a kowace shekara, sun hada da kawar da matsalar nunawa mata wariya, cin zarafinsu da kuma tabbatar da daidaito a tsakanin maza da mata.

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya zukulo wasu daga cikin hotunan yadda aka gudanar da bikin a sassan duniya. A sha kallo lafiya:

Yadda bikin ya gudana a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke New York
Yadda bikin ya gudana a zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke New York
Yadda wasu mata suka gudanar da bikin don nuna goyon baya ga Falasdinawa
Yadda wasu mata suka gudanar da bikin don nuna goyon baya ga Falasdinawa
Yadda wasu mata Aa Tel Aviv suka yi bikin wajen nuna goyon bayan a saki mutanen da Hamas ta kama
Yadda wasu mata Aa Tel Aviv suka yi bikin wajen nuna goyon bayan a saki mutanen da Hamas ta kama
Yadda mata suka yi bikin a Caracas, Venezuela
Yadda mata suka yi bikin a Caracas, Venezuela
Bikin ranar mata a China
Bikin ranar mata a China
Yadda gidan talbijin na Arewa 24 ya gudanar da bikin ranar mata ta duniya (Hoto: Facebook/Dinat Dama Maji)
Yadda gidan talbijin na Arewa 24 ya gudanar da bikin ranar mata ta duniya (Hoto: Facebook/Dinat Dama Maji)

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG