Takaddama kan matsalar tsaro a kudanchin Kaduna dai ta biyo bayan rahoton da ma'aikatar tsaro ta fitar na watanni ukun farkon wannan shekarar, abun da al'umar Atyap su ka ce babu adalci a ciki.
Shugaban Kungiyar Atyap ta Katafawa dake karamar hukumar Zangon Kataf, Mr. Samuel Achi ya kira taron manema labarai inda yayi zargin cewa rahoton tsaron ya nuna yana goyon bayan Fulani.
Achi ya ce an dade ana kashe manoman Zangon Kataf amma ba a daukar mataki kuma bafulatanin da aka kashe a kwanakin baya ma barna ya yi a gona kuma shugabanni sun ba da hakuri sannan su ka alkawarin kamo masu laifin da hannun su.
Sai dai kuma, shugaban kungiyar Fulani ta Miyatti Allah na jahar Kaduna, Alh. Haruna Usman Tugga, ya ce matsalar hare-haren ramuwar gayya ce ta hana rikichin karewa.
Tugga ya ce Katafawa ne ke daukar doka a hannunsu duk lokachin da shanu su ka yi barna a maimakon kai kara wajen hukuma wanda ya ce hakan ke kawo koma baya a dukkan yunkurin kawo karshen matsalar tsaron da ake fama da shi a yankin.
Birgediya Janar Timothy Opurum, shine Kwamandan Operation Safe Haven, da ke kula da harkar tsaro a Kudanchin Kaduna ya kuma sheda cewa bai taba daukar bangare ba gameda matsalar tsaron yankin.
Janar Opurum ya ce zai tabbatar da daukar mataki akan duk wanda ya taka doka ta hanyar kai harin ramuwa; ko bafulatani ne ko bakatafe ba tare da nuna bangaranci ba.
Masana tsaro sun sha nanata bukatar ganin an kawo karshen hare-haren ramuwar gayya tsakanin Fulani da wasu al'umomin kudanchin jahar Kaduna wanda su ka ce shine dalilin da ya hare-haren su ka ki ci- su ka ki cinyewa.
A saurari cikaken rahotun Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5