Ra’ayin Matasa Kan Dimokaradiyya a Adamawa

Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Adamawa Bala Bulus Ngilari.

Kamar yadda akaji dai Wata kotun tarayya dake Abuja akarkashin mai shari’a Adeniyi Ademola tayi umarnin ayi maza a rantsar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Adamawa Bala Bulus Ngilari a matsayin gwamnan jihar mai riko, wanda tun jiya aka rantsar dashi.

Mai shari’a Ademola yafadi hakane alokacin da yake yanke hukunci akan karar da tsohon mataimakin gwamnan ya shigar inda ya nemi a rantsar dashi akan matsayin Gwamnan mai riko har yagama wa’adin toshon Gwamnan jihar Adamawan Murtala Nyako, da aka tsige a ranar goma shabiyar ga watan bakwai na wannan shekara.

To akan wannan batunne na tuntubi shugaban matasa a Kano Anas Saminu Ja’en Makera, shin me irin wannan yake nunawa ko yake koyawa matasan mu ga dimokaradiyya da siyasa a Najeriya Mallam Anas yayi dai yace “wanan yana nuna yadda akewa demokaradiyya hawan kawara a Najeriya, kuma kamata yayi abawa al’uma damar zaben ra’ayinsu ba wai ra’ayin cip joji ba.”