Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra’ayin PDP akan Rantsar da Niglari


Mukaddashin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.
Mukaddashin gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri.

Larabannan ne aka samu sauyin gwamna a Jihar Adamawa, inda aka rantsar da Bala Ngilari a matsayin sabon gwamnan Jihar. Yanzu haka Mr. Ngilari ya maye gurbin kakakin majalisar dokokin kasar, Umaru Fintiri wanda ke rike da wannan mukami a baya.

Sashen Hausa na Muryar Amurka, ta bakin Aliyu Mustaphan Sokoto ya tuntubi Sakataren Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa, Barrista Tahir Shehu domin jin yadda ake ganin wannan batu.

Barrista Shehu yace “wannan abu bai bani mamaki ba, domin tun lokacin da aka tsige shi tsohon gwamna da mataimakinsa, mataimakin wanda Lauya ne, a take ya shigar da kara, yana neman a kalubalanci tsige shi da aka yi, saboda ba’a bi ka’ida ba. Tun daga wannan lokaci aka shiga Kotu, sai jiya Allah Ya kawo karshen wannan shari’a.

Da yake mutane da yawa sunyi mamakin abu biyu, na farko, wannan hukunci, na biyu shine saurin rantsar da Bala Ngilari.

“Abunda nake so mutane su fahimta”, inji Mr. Tahir “kara ya kasu kashi kashi. Akwai karar da mutum zai shigar, yana neman bayani daga kotu. Akwai kuma kara wadda ta shafi hakki, wanda yake bukatar shaida. Karar farko ne aka shigar a wannan lamari, wanda baya bukatar bata lokaci idan aka yanke hukunci. Saboda haka umarnin kotu aka bi, domin zuwa a rantsar da shi nan take."

XS
SM
MD
LG