DAKAR, SENEGAL - Haka kuma yayin da a cikin gida ‘yan hamayya suka tayar da tarzoma da nufin kalubalantar wannan al’amari da suke fassara shi a matsayin juyin mulki.
Dambarwar da ta taso a tsakanin Majalissar Dokokin Senegal da kotun tsarin mulkin kasar dangane da zargin cin hanci a yayin ayyukan tantance ‘yan takarar da suka cancanci shiga zabe ya sa Shugaba Macky Sall dage wannan fafatawa da ya kamata a yi a ranar 25 ga watan nan na Fabrairu kamar yadda ya sanar a jawabinsa na ranar Asabar 3 ga watan Fabrairu.
Hakan ya faru ne sa’o'i kadan kenan kafin a fara yakin neman zabe matakin da ya haddasa zanga zangar ‘yan adawa.
Jingine ranar zabe a wani lokacin da daukacin ‘yan kasa ke zumudin halartar runfunan zabe mataki ne da ka iya haddasa rudani a kasar da a baya ta yi fice kan batun darajta dimokradiya inji Dr. Abba Sedick ‘dan jarida kuma jami’i a cibiyar nazari da bincike kan lamuran yankin Sahel CIRES.
Shugaban kasar ta Senegal ya nanata cewa ba shi da niyyar tazarce to amma ganin yadda ya ayyana bukatar a kira wani taron tattaunawa a tsakanin rukunonin jama’ar kasar ya sa aka fara hasashen yiwuwar ba za a rasa wata manufa a boye ba tattare da abin.
A wata takaitacciyar sanarwa da ta fitar kungiyar CEDEAO ta bayyana cewa ta na bin diddigin abubuwan da ke wakana a Senegal.
Wasu majiyoyi na daban na alakanta wannan yunkuri na canza jadawalin zaben Senegal da kace-nacen da ke tsakanin shugabanin jam’iyun kawancen da ke mulki wato masu goyon bayan ‘dan takarar wannan kawance Firai Minista Amadou Ba da wadanda ke adawa da shi.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5