QATAR 2022: Amurka Ta Kwace Shafukan Yanar Gizo 55 Da Suke Watsa Gasar Cin Kofin Duniya Kai Tsaye Ba Bisa Ka'ida Ba

Amurka ta rufe gidajen yanar gizon 55

Sanarwar da ma'aikatar shari'ar Aurka ta fitar ta ce, an kwace shafukan yanar gizon 55 ne bayan da wani wakilin FIFA ya gano wuraren da ake amfani da su wajen watsa wasan ba tare da izinin hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya ba.

Hukumar FIFA kadai ke da izini na musamman na gasar cin kofin duniya, wanda a yanzu haka ya kai matakin wasan kusa da na karshe.

"Yayin da mutane da dama za su yarda cewa irin waɗannan gidajen yanar gizon ba su zama barazana sosai ba, take hakkin wadanda aka basu izinin watsa wasannin dake zama mallakin su, babbar barazana ce ga ci gaban tattalin arzikinmu," in ji wakili na musamman James Harris na Sashen Tsaron Cikin Gida.

"Za a ga tasirin wannan matakin a cikin masana'antu da dama, yana kuma iya zama wata hanyar aikata laifuka," in ji Harris.

Ma’aikatar shari’ar ba ta bayyana gidajen yanar gizon da aka kwace ba amma ta ce za a karkatar da maziyartan wuraren zuwa wani shafin domin samun karin bayani.