Hanyoyin sadarwa na yanar gizo ba’a barsu a baya ba wajen sada zumunci, fadakarwa, ilmantarwa, kai uwa uba sanarwa. A wannan zamani da muke ciki hanyoyin sadarwa na yanar gizo suna taka rawa matuka fiye da tunanin dan’adam.
Ganin cewar ada abubuwa kan faru a wasu wurare amma baza’a iya sani ba har sai ya dauki lokaci wanda idan gidajen radiyo da talabijin basu dauka ba to haka jama’a zasu zama cikin duhu. Amma yanzu wannan yanar gizon naba ma al’uma dammar sanin meke wakana a wasu bangarorin jihohi da ma duniya baki daya cikin kankani lokaci.
Don haka yakamata al’uma suyi amfani da wadannan hanyoyin sadarwar ta yadda yakamata ba tare da haddasa fitutunu cikin al’umah ba. Wani karin haske da wannan hanyoyin sadarwar suka kawo shine, na yada zumunci cikin kankanin lokaci kuma batare da tsada ba, wanda mutane kan dauki hotuna da bidiyo na abubuwan da sukanyi ko ke faruwa a yankunansu su aika wa sauran dangi a ko’ina. Wannan yasa ana kara samun saukin tafiyar da rayuwa cikin sauki a ko ina a duniya.