Polio Zata Zamo Tarihi A Jihar Sokoto - Wamako

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako na Jihar Sokoto yace yanzu watanni 8 ke nan ba a samu bullar cutar ko sau daya ba a jihar
Gwamnan Jihar Sokoto yace da ikon Allah, sun yi kusan ganin bayan cutar Polio ko shan inna, mai nakkasa yaro ko kashe shi, daga jihar baki daya.

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako yace yanzu watanni 8 ke nan ba a samu rahoton bullar cutar Polio ko sau daya ba a Jihar Sokoto. yace wannan ba zai rasa nasaba da yadda suka dage wajen rigakafi ba, da kuma yadda ake samun hadin kan uwayen kasa, kama tun daga kan Mai Alfarma Sarkin Musulmi har zuwa kan sauran sarakuna, da kuma malamai da jama'a, wadanda duk ke ba gwamnati hadin kai wajen cimma wannan gurin kawar da cutar.

Gwamnan yace akasarin bullar cutar da aka samu a baya ma tana da nasaba ne da matafiya dake shiga jihar daga wasu wurare, yana mai cewa babu yadda za a iya hana matafiya shiga jihar, kuma babu yadda za a ce sai wadanda suka yi rigakafi kawai zasu shiga.

Gwamnan ya roki al'ummar Jihar Sokoto da su bayar da cikakken hadin kai domin tabbatar da cimma wannan gurin.

ga bayanin da gwamna Wamako yayi a tattaunawarsa da wakilin sashen Hausa, Saleh Shehu Ashaka.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamna Aliyu Magatakarda Wamako Na Sokoto Kan Polio - 1:04