A shekara ta 2010, gwamnatin tarrayya ta kirkiro da wani shirin mata masu kiwon lafiya, aka kuma dauki fiye da 4,000 unguwar zoma aiki aka tura su dakunan magani dubu 1,000 dake fadin kasar. Bisa ga rahoton, kula da lafiyar mata masu ciki zai iya cetar rayuka, kamar yadda samun kula mai kyau lokacin ciki yake da mahimmanci ga lafiya, rayuwar iyaye mata da kuma jariransu.
Ziyarar masu ciki ta hada da allurar rigakafi, binciken sauran cututtuka, da kuma gane alamun lokaci ya kusa na haihuwa.
A lokacin wannan ziyarar, ake gwada mata masu ciki kan cutar kanjamau; idan suna da ita, zasu sami taimakon magani da shawarwari kan yadda zasu kare lafiyarsu da ta jariran da suke dauke da su.
A Nigeriya, ana fara wannan ziyara a farkon mako 14 na daukar ciki. Idan mai ciki ta fara zuwa awo bayan ta wuce makonni 14 za a ce ta fara zuwa da latti.
Masana sunce zuwa ziyarar mata masu ciki da wuri da kuma ziyara kowanne lokaci, yana taimakon mata da ‘ya’yansu sosai. Yana kawo ilimi da shawarwari akan irin sakewar da ake samu lokacin ciki, abinda ke kawo su, da kuma matsalolin da zasu iya zuwa lokacin ciki, lokacin haihuwa da sauransu.