Gwamnati tayi haka ne ta wurin kaddamar da kwamitin mutum 12 na shugaban kasa a kan shirin lafiya na gaba daya karkashin jagorancin Mrs Fatima Bamidele, ta ma’aikatar lafiya.
Kwamitin zai shirya yadda aiki zai ci gaba a sashin lafiya, kuma an bashi tsawon wata hudu ya bada ruhotonsa.
A ranar kaddamar da wannan kwamiti, ministan lafiya, Prof. OnyebuchiChukwu yace, Mahimmin sakamakon da ake bukata daga wannan kwamiti shine hanyar da za’a bi domin tanada shirin lafiya ga dukan ‘yan Nigeriya a hanyar da zata iya iske kowa.
Sauran shirye shirye na bada lafiya suna karkashin shirin SURE-p da kuma shirin save one million live initiatives.