Dr. Nisser Aliyu Umar, shugaban hukumar, yace a bana, babu inda cutar Polio ta yi tsanani kamar yankin Arewa Maso Gabas, musamman a saboda rashin kwanciyar hankali a jihohin dake wannan yanki. Yace jihohin Borno da Yobe, inda aka fi fama da fitina, nan ne kuma cutar ta fi tsanani.
Amma Dr. Umar yace an samu sabbin kamuwa da cutar Polio guda 4 a Jihar Bauchi ya zuwa wannan lokaci a cikin shekarar nan. Yace a dalilin haka ne ya sa yanzu a kowane wata, ma'aikatan asibiti a Jihar su kan shiga cikin garuruwa da kauyuka su kakkafa tebura su na bayar da maganin rigakafin, maimakon su jira har sai lokutan da ake kaddamar da kyamfe na yaki da wannan cuta.
Ya ja kunnen ma'aikatan hukumar dake bayarda wannan maganin da su kasance masu mutunta jama'a da halin kwarai, yana mai rokon jama'a da su ba da jami'an hadin kai domin raba Jihar Bauchi da ma Najeriya da wannan cuta ta Polio.
Wakiliyarmu Amina Abdullahi Girbo, ta aiko da karin bayani kan wannan.