PDP ta Baiwa Shugaba Buhari Wa’adin Kwanaki Goma

Shugaba Muhammad Buhari

Babbar jami’iyyar adawa a Najeriya PDP, ta kara chachakara Gwamnatin Muhammadu Buhari, da tana nemar fakewa da cewa Gwamnatin Jonathan ce ta rikita lammura da ya sanya rashin shiga aikin Gwamnati ka’in da na’in.

Tun farkon mako dai PDP, tace Buhari na bukatar Adu’ar ‘yan Najeriya, don tafkar ya amshi ragamar kasa ce da ya rasa ta inda zai fara aiki, kuma wata daya Kenan a cewar PDP, sabuwar Gwamnatin bata cimma komai ba sai romon baka.

Sakataren labaran PDP, Olisa Metu, yace Gwamnatin APC, na sharara zukitamale da jefa demokradiyar Najeriya , a wani garari, gaskiya sun fara sakar da mumunar zare, PDP, dai ta baiwa shugaba Buhari wa’adin kwana goma da ya nada majalisar sa ta zartarwa.

Take fadar shugaban kasa ta nuna a yanzu tana aiki share ta’anatin da PDP, ta yiwa Gwamnati ne. Wata majiya ta bayyanawa wakilin muryar Amurka , Nasiru Adamu Elhikaya, cewa Gwamnatin Buhari, ta gano Gwamnatin da ta shude bar bashin Naira Tiriliyon bakwai a baitulmalin da idan anyi lissafi ba komai.