Paris 2024: Djokovic Ya Kai Wasan Kwatai-Fainal

Novac Djokovic

Dan kasar Serbia Novak Djokavic ya kafa tarihin kai wasan kwata-fainal na wasan tennis a gasar Olympics karo hudu a jere, bayan da ya doke dan kasar Jamus Dominic Koepfer da ci 7-5; 6-3 a ranar Laraba.

Ga dukkan kofinan Grand Slam 24 da ya lashe da wasu lambobin yabo marasa adadi, dan wasan mai shekaru 37 bai taba lashe gasar Olympics ba, wanda lambar tagulla ta kasance abin tunawa da shi kadai.

Watakila wasan Paris ya zama shi ne dama ta karshe don cike gurbi daya na kofunansa da ya lashe, kuma ya zuwa yanzu komai yana tafiya daidai kamar yadda aka tsara a gasar Roland Garros saboda har yanzu bai yi rashin nasara ba a zagaye uku na wasan.

Bayan jin dadi da fargaba na nasarar da ya yi a wasan da ya buga da babban abokin hamayyarsa Rafa Nadal, yanayin damuwa a filin wasan Philippe Chatrier ta tafi, yayin da a cikin nutsuwa ya yi waje da Koepfer mai shekaru 30 bayan da a farko ya samu matsala.

Koepfer da ya samu kwarin gwiwa bayan ya yi nasara sau hudu a wasan mutun daya da na mutum biyu zuwa yanzu a wasan tennis na Olympics a Roland Garros, bayan da bata rawarsa da tsalle da yake kasa da 5-6, yayin da ya buga kwallon da karfi da ya yi kuskure ya bai wa Djokovic damar lashe zagayen.

An duba lafiyar Bajamushen a farkon zagaye na biyu na wasan kuma kokarinsa ya ragu nan take yayin da Djokovic ya yi nasara ta 16 a wasan mutun daya a gasar Olympics, wadda itace mafi yawa da wani dan wasa ya samu tun bayan dawo da wasan tennis a wasannin a 1988.

Djokovic zai buga wasa na gaba da dan kasar Girka kuma na takwas a duniya Stefanos Tsitsipas, wanda ya kai kwata-fainal bayan da ya doke dan kasar Argentina Sebastian Baez.

Reuters