Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Paris 2024: 'Yan Sandan Faransa Suna Karfafa Tsaro Saboda Kasashe Masu Adawa Da Juna


Football - Men's Group D - Israel vs Paraguay
Football - Men's Group D - Israel vs Paraguay

Shugaban tawagar ‘yan wasan kasar Iraqi ya ce shugabannin Olympics sun yi watsi da bukatar su cewa kada a cira tutar Isra’ila a kusa da ta Iraqi a lokacin wasannin Paris.

Kungiyar kwallon kafar maza ta Iraqi ta lallasa Ukraine da ci 2-1 a birnin Lyon a ranar Laraba kana ta sha kashi a hannun Argentina da ci 3-1 a yau Asabar.

“Yayin da muka isa filin wasa na Lyon a ranar Laraba, mun ga an kafa tutar Iraqi kusa da ta Isra’ila,” duk da cewa kungiyar Isra’ila bata da wani wasa da zata yi a Lyon, in ji Herda Raouf, yana fadawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.

Raouf, wanda bai yarda da hallacin kasar Isra’ila ba kuma yake marawa kasar Falasdinu baya, ya kara da cewa tawagarsa ta bukaci wakilin kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya (OIC) da ta sake wa tutar Isra’ila wuri amma an yi buris da bukatar su.

A cewar Raouf, wakilin na kwamitin ya ce an shirya tutocin kungiyoyin ‘yan wasan kwallon kafar mata da mazan ne bisa tsarin harafin fari na kowace kasa.

Raouf ya kara da cewa, tawagarsa ta kara tura kin amincewarta a hukumance ta sakon imel zuwa ga IOC a kan bukata wannan kafin wasanta da Argentina, amma aka kuma sake fatali da ita.

Dakarun tsaron Faransa suna kallon wasan Ukraine da Iraqi da kuma wasan Isra’ila da Mali da aka yi su a ranar Laraba a matsayin masu tattare da hadari.

Kimanin jami’an ‘yan sandan Faransa dubu daya ne aka jibge domin bada tsaro a wasan Isra’ila da Mali, inda ‘yan kallo su ka daga tutar Falasdinu da ta Irsa’ila.

Kwamitin Olympic na kasar Falasdinu sun rubutawa IOC a makon da ya gabata cewa ta hana ‘yan wasan Isra’ila shiga gasar Olympics a Paris saboda yakin Gaza, bukatar da aka yi fatali da shi.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG