Paparoma Francis Ya Kafa Sabuwar Doka

Paparoma Francis, ya samar da wata doka wacce ta nuna cewa daga yanzu, duk wani Bishop da aka samu ya yi sakaci, yayin saurarar wani korafi kan wani Malamin addinin kirista da ake zargi da cin zarafin kananan yara zai bar mukaminsa.

Wannan sabuwar doka da fadar ta Vatican ta fitar a yau Asabar, martani ce ga kiran da masu rajin kare darikar katolika a Amurka ke yi, wadanda suka nuna cewa cocin na gazawa wajen daukan matakai akan malaman addinin kirista masu lalata da kananan yara.

Dokar har ila yau ta yi nuni da cewa har Bishop Bishop wadanda ba sa lura da mabiyansu, aka kuma samu irin wannan lalata a karkashin jagorancinsu, suma za su bar mukaminsu.

A baya wasu daga cikin yara kananan da aka ci zarafinsu sun yi zargin cewa, a Amurka akwai Bishop Bishop da ke yin rufa-rufa ga irin wannan matsala koda sun san tana faruwa.