Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararren Dan Damben Amurka Muhammad Ali Ya Rasu


Muhammad Ali
Muhammad Ali

Fitattun 'yan wasa na cigaba da aikawa da sakkonin ta’aziyya da nuna alhini daga sassan daban daban na duniya, dangane da rasuwar shahararren tsohon dan wasan damben zamanin Amurka Muhammad Ali, wanda ya rasu a daren jiya Juma'a a wani asibiti da ke Phoenix a jihar Arizona.

Muhammad Ali ya rasu ne yana mai shekaru 74 kewaye da iyalansa, bayan da ya kwashe wasu ‘yan kwanaki yana karbar maganin wata cuta mai nasaba da hanyoyin numfashi.

Ya kuma kwashe shekaru 32 yana fama da cutar Parkinson mai sa kakkarwa, wacce aka gano yana dauke da ita a shekarun 1980s.

Ali mutum ne da aka nunawa kauna matuka a duniyar damben zamani, inda ta kaiga har mujallar dambe nan ta Sports Illustrated ta nada shi a matsayin fitaccen dan wasan karni na 20.

Muhammad Ali mutum ne da aka mai kallon mai yawan cika baki da kuma basirar iya sarrafa kalamomi yadda ya ke so, kamar fitacciyar maganar nan da ya taba yi cewa: “shi yana tashi kamar Malam bude mana littafi , yana kuma harbi kamar zuma.”

A haife shi ne a birnin Kenturkey, kuma mahaifinsa sana’ar penti ya ke yi a lokacin, ya kuma tsunduma cikin harkar dambe ne bayan da wasu ‘yan unguwarsu suka sace mai keke.

Ya canza sunansa daga Cassius Clay zuwa Muhammad Ali a ranar shida ga watan Maris din shekarar 1964 bayan da ya karbi addinin Islama.

XS
SM
MD
LG