Prime Ministan Pakistan Yusuf Reza Gilani ya yiwa Amirka kashedin cewa, tilas ta kawo karshen shafawa kasarsa kashin kaji da take yi ta hanyar zargin Pakistan da laifin goyon bayan hare haren day an yakin sa kai ke kaiwa Afghanistan. Yace irin wadannan zarge zarge babu abinda zasu haifar, illa kara cusa tsanar Amirka a zukatan ‘yan kasar.
Prime Ministan na Pakistan, ya yi wannan furucin ne a wata hira da kamfanin dilancin labarum Reuters yayi dashi. Yace barin Amirka ta dauki matakin farautar yan yakin sa kan kungiyar Haqqani salon wanda tayi amfani dashi a sumamen data kashe shugaban kungiyar Al Qaida Osama Bin Laden a watan Mayu, zai zama keta ka’idar diyaucin kasarsa ne.
Mr Gilani yayi wannan furucin ne, kwana daya bayan da rundunar sojan Pakistan tace ba zata auna yan kungiyar Haqqani da aka ce tana da alaka da kungiyoyin Al Qaida da Taliban ba, a saboda tuni aiki yayi mata yawa a fafatawa da ‘yan yakin sa kai da take yi a yankin arewa maso gabashin kasar.
Haka kuma a jiya Talata daruruwan yan Pakistan ne suka yi gangami a duk fadin kasar domin nuna wa take taken Amirka rashin amincewa.