Shugaban yankin Falasdinu Mahmud Abbas, ya gayawa dubban magoya bayansa a birnin Ramallah dake yammacin kogin Jordan cewa suna daga cikin “rundunar juyin juya hali na Falasdinawa”, kuma zai koma teburin shawarwari ne kawai idan Isra’ila ta tsaida gine gine a yankuna da ta mamaye.
Jiya lahadi Mr. Abbas ya sami kyakkyawar tarba da komawarsa yammacin kogin Jordan daga New York, inda ya gabatar da bukata ga majalisar dinkin duniya na neman amincewa yankin, a matsayin kasa mai cin gashin kai.
Yau litinin ake sa ran kwamitin sulhu na majalisar dinkin Duniya zai fara zama kan bukatar da yankin na Falasdinu ya gabatar.
Da yake magana ta tashar talabijin ta NBC anan Amurka jiya lahadi, Firai Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu yace bukatar da yankin ya gabatar bai dace ba, kuma bai kamata ace ta sami amincewa ba domin bisa ga cewarshi, yankin na Falasdinu yana son samun ‘yancin kai ba tare da bada tabbaci kan tsaron Isra’ila ba.
Ya sake nanata kira da ya yiwa falasdinawa na dawowa teburin shawarwari nan take ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
Amma wata jigo daga yankin na Falasdinu Hanan Ashrawi, ta maida martani nan take da take magana ta tashar talabijin ta ABC. Tace Isra’ila tana son ta kama birnin kudus baki daya, ta kuma kauda batun ‘yan gudun hijira cikin ajendar shawarwari. Tace Isra’ila tana son ta mallaki komi, san nan daga bisani tace to yanzu kuzo mu tattauna.