Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firai Ministan kasar Pakistan ya bayyana gaban kotun koli


Firai Ministan kasar Pakistan Yousaf Raza Gilani
Firai Ministan kasar Pakistan Yousaf Raza Gilani

kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani ya bayyana gaban kotun kolin kasar domin kare kanshi bisa zargin watsi da doka. PM kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani ya bayyana gaban kotun kolin kasar domin kare kanshi bisa zargin watsi da doka. PM kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani ya bayyana gaban kotun kolin kasar domin kare kanshi bisa zargin watsi da doka.

PM kasar Pakistan Yusuf Raza Gilani ya bayyana gaban kotun kolin kasar domin kare kanshi bisa zargin watsi da doka.

Gilani ya isa kotun yau alhamis karkashin cikakken tsaro domin kare shawarar da ya yanke ta kin kira ga hukumomin kasar Switzerland su bincike zargin sama da fadi da ake yiwa shugaban kasar Asif Ali Zardari.

Mr. Gilani yace shugaba Zardari yana da kariya a matsayinshi na shugaban kasa.

Kotun ta janye zamanta sai farkon watan Fabrairu, abinda zai ba PM mako biyu ya shirya kare kanshi. Sai dai kotun ta ce baya bukatar bayyana gaban kotun da kanshi nan gaba.

Idan aka sami PM da laifi za a iya yanke mashi hukumcin dauri ya kuma rasa mukaminshi.

Ana kara matsawa shugabannin farin kayan Pakistan lamba, wadda take fuskantar shari’u a kotuna da kuma zaman doya da manja tsakaninta da rundunar sojin kasar mai ikon fada a ji. Dangantaka tayi tsami ainun tsakanin shugaba Zardari da babban alkalin kasar.

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG