Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majiyu a Saudiya sun ce Sarki Abdullah ya soke hukumcin da aka yankewa wata mace direba


Wata mace tana tuka mot a kasar Saudiya.
Wata mace tana tuka mot a kasar Saudiya.

Majiyu a gwamnatin kasar Saudiya sun ce sarki Abdullah ya soke hukumcin da wata kotu ta yanke na yiwa wata mace a kasar bulala goma sabili ta kalubalantar dokar hana mata tuki da masarautar ta kafa

Majiyu a gwamnatin kasar Saudiya sun ce sarki Abdullah ya soke hukumcin da wata kotu ta yanke na yiwa wata mace a kasar bulala goma sabili ta kalubalantar dokar hana mata tuki da masarautar ta kafa.

Daya daga cikin wadanda suka sanar da shawarar da sarkin ya yanke ita ce ‘yar sarki Amira al-Taweel wadda ta rubuta a shafin sadarwarta na Tuitter. Babu wani tabbaci daga gwamnati.

Ranar Talata wata Kotu a birnin Jidda ta sami Shaima Jastaina da laifin keta dokar tuki. Hukumcin ya ba matan Saudiya mamaki, kasancewa yazo kwana daya bayanda sarki Abdullah ya sanar da cewa za a ba mata ‘yancin kada kuri’a da tsayawa takara daga shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Kungiyar kare hakkin bil’adama Amnesty International tayi na’am da sabuwar dokar ‘yancin kada kuri’a sai dai ta bayyana ranar Talata cewa, garambawul din da sarkin zai yi ba zai zama da ma’ana ba, muddar za a ci gaba da tuhumar mata sabili da yin amfani da ‘yancinsu na walwala. Kungiyar kare hakin bil’adaman tace akwai kuma rahotannin wadansu mata guda biyu da ake tuhuma da laifin tuki a masarautar.

Babu wata rubutacciyar doka a kasar Saudiya da ta haramtawa mata tuki, sai dai fatawa.

A da, ‘yan sanda sukan tsaida direbobi mata su yi masu tambayoyi daga nan su kyale su su tafi, bayan sun yi alkawari a rubuce ba zasu kara tuki ba. Sai dai mata da dama sun shiga tuki tun daga watan Yuni a kamfen da suke yi na keta wannan doka. Wannan ya janyo kama mata da dama.

Kasar Saudiya ce kasa daya rak a duniya da aka haramtawa mata tuki, dokar da ta shafi mata ‘yan asalin kasar da kuma baki.

XS
SM
MD
LG