Ohanaeze Ta Bukaci Tinubu Ya Saki Nnamdi Kanu Don Zaman Lafiya

Shugaban APC Bola Tinubu

Shugaban APC Bola Tinubu

Yayin da Najeriya ke kara kusantowa ga ranar 29 ga watan Mayu da za a rantsar da sabon shugaba kasa, kungiyar Ohanaeze Ndigbo, a ranar Laraba, ta fitar da wasu bukatu hudu ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, ya cika domin kwantar da hankalin ‘yan kabilar Igbo.

Babban Sakataren kungiyar Ohanaeze, Okechukwu Isiguzoro, ya ce ya kamata Tinubu ya saki Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, ba tare da wani sharadi ba.

Isiguzoro ya ce sakin Kanu zai dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin Kudu maso Gabas.

Ya yi nuni da cewa, dole ne Tinubu ya tabbatar da yankin Kudu maso Gabas ya samar da shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra,

Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra,

Da yake magana da Jaridar Daily Post da rawaito wannan labari, jigon na Ohanaeze ya ce dole ne Tinubu ya tabbatar da ganin an kirkiri jiha ta shida a yankin kudu maso Gabas.

A cewar Isiguzoro: “Tinubu mai son ci gaba ne, shi mai dabara ne; gwamnatin Tinubu ba za ta zama kamar gwamnatin Buhari ba.

“Matsalar Tinubu ita ce yawan shekaru, da kuma mafi yawan mutanen da suka sa Buhari bai yi nasara ba suna bayansa saboda wasu kalubalen da ya ke fuskanta biyobayan zaben shekarar 2023.

“Dole ne Tinubu ya tabbatarwa da yankin Kudu maso Gabas wadannan muhimman bukatu hudu don yankin ya amince da shi a matsayin shugaban Najeriya, kana kabilar Igbo su tsaya tsayin daka su kare mulkinsa.

Nnamdi Kanu da lauyoyinsa a zaman kotun da aka yi a ranar Alhams (Channels TV)

“Na farko shi ne, dole ne Tinubu ya maido da zaman lafiya da tsaro ba tare da wani sharadi ba ta hanyar sakin Nnamdi Kanu, ko zai ba shi afuwar shugaban kasa daga dandalin Eagles Square a lokacin jawabin karbar mulkin sa ko kuma ya yi amfani da karfin ikon shugaban kasa wajen ganin an sake shi domin dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin kudu maso gabas.

“Na biyu, dole ne Tinubu ya fara aikin warkarwa wurin ganin ya daidaita tikitin Musulmi da Musulmi a takarar shugaban kasa ta hanyar bai wa Kirista daga Kudu maso Gabas shugaban majalisar dattawa. Duk wanda zai zama Shugaban Majalisar Dattawa kada ya zama wani sanata mai mukami a majalisar wadanda ba shi da kishin kasa.

"Muna kira ga majalisar dattijai da ta gyara dokokinta tare da ba da izinin sababbin ‘yan majalisa su jagorancin gidan saboda sanatocin da ke rike da mukamin akwai shakku a kan su kuma ba za su iya kare muradun Ndigbos (kabilar Igbo) ba.

“Na uku, dole ne Tinubu ya sanya tsarin siyasa da zai tabbatar da cewa ‘yan kabilar Igbo sun ga alkawarin da Buhari ya yi masu a asirce cewa zai tabbatar da yankin ya samu jiha ta shida; Ohanaeze ya riga yana da shirinsa.

“Dole ne zababben shugaban kasa ya tabbatar da cewa dukkan kofofin tattalin arziki a fadin kasar nan da suka hada da sake bude mashigar ruwa ta Calabar, yaye kogin Azumiri, yiwa ‘yan kungiyar IPOB afuwa, da kuma biyan diyya ga iyalan da aka kashe tsawon shekaru.”