Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamin Ministan Man Fetur Na Najeriya Timipre Sylva Ya Yi Murabus - Majiyoyi


Karamin Ministan Man Fetur Na Najeriya Timipre Sylva
Karamin Ministan Man Fetur Na Najeriya Timipre Sylva

Karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya yi murabus daga mukaminsa a kasar domin neman sabon wa'adi a matsayin gwamnan jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a yankin Neja Delta.

Wasu majiyoyi a ma'aikatarsa da suka bukaci a sakaya sunansu suka shaida mana da maraicen ranar Alhamis.

Murabus din Sylva na zuwa ne kwanaki 60 kacal, kafin wa’adinsa a kan mukamin karamin ministan albarkatun mai ya kare kuma a daidai lokacin da ake shirin kafa sabuwar gwamnati a Najeriya, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari ke makonninsa na karshe a kan karagar mulki kafin ya mikawa zababben shugaban kasa Bola Tinubu mulki a ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa.

Rahotanni dai sun yi nuni da cewa, Timipre Sylva ya mika wa shugaba Buhari da kuma babban ministan albarkatun man fetur takardar murabus dinsa ne tun a makon da ya gabata, kuma tuni ya daina zuwa ofishin, in ji wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.

Muhammadu Buhari
Muhammadu Buhari

Haka kuma, wata majiya ta yi nuni da cewa, Sylva zai nemi tikitin takara karkashin inuwar jam’iyyar APC mai mulki, don tsayawa neman kujerar gwamnan Bayelsa a zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Afrilun mai kamawa.

Tsakanin shekarar 2008 zuwa 2012, Timipre Sylva ya dare kujerar gwamnan jihar Bayelsa na tsawon wa'adi daya tak a karkashin inuwar jam'iyyar PDP mai mulki a matakin tarayya a waccan lokaci, amma a yanzu yana jam’iyyar adawa a jiharsa.

Idan ana iya tunawa, a watan Agustar shekarar 2019 ne aka nada Sylva a matsayin karamin ministan albarkatun man fetur, inda ya jagoranci manyan sauye-sauye a fannin mai wadanda suka hada da zartar da dokokin da suka yi wa tsarin kasafin kudin sashen kwaskwarima a wani yunkuri na karfafa zuba jari.

A lokacin da yake rike da mukamin minista ne aka ga raguwa matuka a yawan man da Najeriya ke hakowa a cikin shekaru da dama da suka gabata, sakamakon satar danyen mai da fasa bututu da wasu baragurbin mutane ke yi.

Daga bisani kasar Angola ta zarce Najeriya a matsayin kasar da ta fi fitar da man fetur a nahiyar Afirka na wasu watanni a bara.

Duk kokarin ji ta bakin Timipre Sylva a yayin rubuta wannan labari ta hanyar kiran wayan tarho dai ya ci tura kuma ma’aikatar man fetur ta ki cewa komai a kań batun.

XS
SM
MD
LG