Obama Ya Fara Ziyarar Kenya Da Habasha

Kenya Attack Obama

Shugaban Amurka Barack Obama ya fara ziyarar aiki a kasashen Kenya da Habasha inda zai tattauna huldar kasuwanci da kasashen biyu.

A yau Alhamis, Shugaban Amurka Barack Obama, ya kama hanyar zuwa Habasha zai kuma dangana da Kenya inda aka haifi mahaifinsa.

Ziyarar na zuwa ne a daidai lokacin da ake danganta habakar tattalin arzikin Amurka da kasashen da ke kudu da Sahara.

A gobe Juma’a zai yada da zango a Kenya inda zai halarci taron koli na ‘yan kasuwar duniya a Nairobi, babban birnin kasar.

Daga baya kuma zai kai ziyara Habasha, wanda hakan zai sa ya zamanto shugaban Amurka na farko da zai kai ziyara kasar.

Kungiyoyin masu kare hakkin bil adama a Habasha, suna sukan ziyarar ta Obama saboda yadda Amurkan ta zira ido tana kallon takaddamar siyasar kasar ba tare da ta ce uffan ba.

A ranar larabar da ta gabata, shugaba Obama ya yi magana kan huldar kasuwanci tsakanin Amurka da Afrika a Fadar White House wanda hakan ya ba da damar saka hanu a wata yarjejeniyar bunkasa tattalin arzikin nahiyar.